Yajin aikin na sai yadda hali yayi na kokawa ne kan wasu bukatu da suka ce suna son gwamnati ta gaggauta cika masu saboda ba zasu janye yajin aikin ba sai an biyasu.
Malam Issoufou Maihatsi magatakardan kungiyar malaman reshen Birnin Kwanni ya shaidawa Muryar Amurka cewar gwamnati tayi masu alkawura da yawa da bata cika ba.
Malaman sun bukaci a sasu su zama ma'aikatan gwamnati na din-din-din kamar sauran ma'aikatan gwamnatin kasar. Maihatsi yace gwamnati tayi alkawarin sasu amma bata sa ba. Sun sa wasu amma akwai na shekaru biyu da suka gabata da basu sa ba. Yanzu haka suna bin gwamnatin bashin wasu alkawura wajen shekaru biyu, inji Maihatsi.
Dangane da sa malaman cikin ma'aikatan gwamnati, Maihatsi yace gwamnatin ta fito karara tace ba zata sasu wannan shekarar da ma shekara mai zuwa ba. Baicin haka akwai albashin watanni biyu zuwa ukku da gwamnati bata biya ba. Saboda haka malaman suka tsayar da aiki har sai an biyasu.
A cewar shugaban iyayen 'yan makarantun boko Alhaji Sani Maikaset yace yakamata malaman da gwamnati su ji tsoron Allah saboda yajin aiki a makaranta ci baya ne ba ci gaba ba ne. Kamata yayi a kula da ilimi idan kuma ana wasa dashi to akwai matsaloli, inji Maikaset.
Ga rahoton Haruna Mamman Bako da karin bayani.