Akalla gidaje da wuraren kasuwanci miliyan biyu ne suke ci gaba da zama babu wutar lantarki a yau Lahadi, tun bayan wata mummunar guguwa da ta ratsa gabashin Amurka a ranar Juma’ar da Asabar.
Ruwan sama da dusar kankara hade da guguwar ne suka ratsa ta jihar Maine, inda har gwamnan jihar ya ayyana dokar ta-baci.
Guguwar ta kai har zuwa jihar North Carolina da ke kudancin Amurka.
A jiya Asabar gwamnan jihar ta Maine ya ayyana dokar ta-bacin, kamar yadda takwarorinsa na jihohin Virginia da Maryland suka yi gabanin wannan mataki da ya dauka.
Ya zuwa yammcin jiya Asabar, kamfanin sufurin jiragin kasa na Amtrak, da ya dakatar da zirga zirgarsa, ya koma bakin aiki, ko da yake an samu jinkiri wajen gudanar da ayyukan na sa.
Sannan an soke tashi da saukar jirage da dama a biranen New York da Boston da ke jihar Massachussetts.
Wannan mummunar guguwa ta faro ne tun daga ranar Juma’a, wacce ta yi tafiyar kilomita 145 cikin sa’a, ta kuma haifar da ambaliyar ruwa a titunan Birnin Boston da sauran garuruwan da ke bakin gabar teku.
Rahotannin sun ce, akalla mutane bakwai ne suka mutu sanadiyar faduwar bishiyoyi a jihohin Virginia, Maryland, Pennsylvania, da New York da Connecticut da kuma Rhode Island.
Facebook Forum