Hukumar zabe ta jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaben shugabannin kananan hukumomi da kansiloli a fadin jihar. To amma kungiyoyin rajin tabbatar da shugabancin na gari na bayyana shakku dangane da yadda sahihancin zaben zai kasance. A hannu guda kuma, babbar Jam’iyyar hammaya a jihar wato PDP ta ce ba za ta shiga zaben ba, kuma yanzu haka ta shigar da kara kotun daukaka kara dake Kaduna.
Shugaban hukumar zabe ta Jihar Kano,Farfesa Garba Ibrahim Sheka ya ce kawo yanzu babu wanda ya yi masu katsalandan ko yace ga yadda zasu gudanar da ayyukansu duk da korafin da wasu keyi kuma ya bada tabbacin gudanar da zabe mai inganci.
A zaben na gobe dai, ana sa ran zabar shugabanin kananan hukumomi 44 da mataimakansu da kuma kansiloli 484 a fadin jihar ta Kano.
To amman Jam’iyyar PDP na kauracewa zaben bayan da babar kotun jihar Kano ta kori karar da ta shigar gabanta na kalubalantar hukumar zaben.
Shugaban Jam’iyyar ta PDP a jihar Kano, Sanata Mas’udu El-Jibril Doguwa ya bayyana cewa kudin takardar shiga takarar ya yi yawa. Yace babu yadda wanda ya fito daga karamar hukumar Doguwa a ce sai ya sayar da buhun masara 60 kana ya hada kudin sayen takardar takara. Misali wanda zai tsaya takarar shugaban karamar hukuma zai biya Naira dubu 400.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin rajin demokaradiyya ke bayyana shakku game da yiwuwar ingancin zaben na gobe.
Comrade Kabiru Saidu Dakata, jami’i a cibiyar CITAD ta ci gaban al’umma da dimokradiyya a nan Kano ya ce, "Idan aka yi zabe muka ga abun da aka saba gani a jihohi cewa duk jam’iyyar da ta ke mulki a wannan jiha ita za ta cinye dukkan kujeru to kenan tsarin kananan hukumomi ba da gaske ake yi ba. Baya ga haka, PDP ta daukaka kara kana bangaren Kwankwasiya na kotu saboda haka duk wadannan sun ragewa zaben armashi."
A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani
Facebook Forum