Gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na jihar Kano sunyi Allah wadai da yunkurin Jami’an gwamnatin jihar Kano da sanatocin dake wakiltar jihar a majalisar dattawan Najeriya keyi na dawo da siyasar daba a jihar.
A wani taron manema labarai da suka kira a karshen mako, gayammar kungiyoyin fararen hula dana gwagwarmaya, sunce abubauwan dake faruwa tsakanin tsoho da sabon gwamnan jihar Kano da kuma mukarraban su, bai dace da tsari da akida da kuma tarbiyyar al’umar Kano ba.
Hajiya Aisha Dankani Kenan guda cikin shugabannin kungiyoyin gwagwarmar tabbatar da shugabanci na gari a jihar Kano cikin wadanda suka yi magana.
Ita kuwa Hajiya Hauwa Ibrahim Elyakub, cewa tayi tafarkin da shugabannin gwamnatin Kano da wakilan Kano a majalisar dattawan najeriya suka kama abu ne da ka iya gurbata tarbbiyyar al’uma mai tasowa a jihar.
Masu kula da al’amura dai na ganin cewa, matakin gamayyar kungiyoyin gwagwarmayar na yanzu tamkar fargar jaji ne, to amma comrade Ibrahim Wayya na cewa ba haka lamarin yake ba.
Facebook Forum