Hukumar zabe ta jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen da suka kamata domin gudanar da zaben kananan hukumomin jihar a ranar asabar mai zuwa wato 10 ga wannan wata na Fabareru, a yayin da babbar kotun jihar ta zata sanar da hukuncin ta a ranar Talata dangane da karar da Jam’iyyar PDP ta shigar gabanta tana kalubalantar hukumar zaben.
Hukumar dai tace ta tuni ta dauki ma’aikatan wucin gadi da zasu tallafa mata wajen gudanar da zaben, inda za’a zabi shugabannin kananan hukumomi 44 da mataimakan su da kuma kansilolin 484 a fadin jihar ta Kano.
Sai dai, Jam’iyyar PDP na kalubalantar hukumar zaben a kotu game da kudaden da take karba daga hannun ‘yan takara. To amma Prof Garba Ibrahim Sheka dake zaman shugaban hukumarna cewa.
Kotun dai ta saurari karar a juma’ar nan karkashin jagorancin mai rikon kujerar babban jojin jihar Justice Nura Sagir kuma ta fitar da ranar talatar makon gobe domin yanke hukunci.
a yayin zaman bangarorin biyu sun bada bahasi. Barr Ibrahim mukhtar dake zaman atoni janar kuma kwamishinan shari’a na jihar Kano shine ke kare hukumar zabe.
Anasa bangaren lauyan Jam’iyyar PDP Barr Abdul Adamu na cewa, jam'iyyar ta gabatar da hujjoji da zsu gamsar da kotu kan haramcin kudade da hukumar zaben jahar tke cacin 'yan takara.
Barr Abdul Adamu Fagge Kenan lauyan Jam’iyyar PDP.
Facebook Forum