WASHINGTON, DC —
Yau shirin Domin Iyali yana tare da Barrister Badiha Mu’azu ‘yar gwaggwarmaya kan harkokin mata, daya daga cikin wadanda shirin ya yi hira da su kan bukin ranar 'ya'ya mata ta duniya da ake gudanarwa ranar goma sha daya ga watan Oktoba kowacce shekara. Wakilinmu Mahmud Ibrahim Kwari ya nemi sanin abinda yasa wadansu suke gani kamata yayi a fi bada fifiko kan ilimantar da 'ya'ya mata fiye da sauran batutuwa da suka shafe su sai Barrister Badiha Mu'azu ta bayyana cewa ilimi shine ginshikin ci gaban mata. Tace ilimi zai iya magance dukan matsalolin da mata ke fuskanta. Ga cikakken bayanin.
Facebook Forum