WASHINGTON, DC —
Yayinda ake cika shekaru biyar da sace 'yammatan Chibok, da har yanzu kungiyar Boko Haram da ta sace su take rike da 'yammata dari da goma sha biyu daga cikin 'yammata dari biyu da saba’in da shida da ta sace a makarantar su, kungiyar kuma take ci gaba da rike Leah Sharibu dalibar makarantar sakandaren garin Dapchi bayan sakin sauran dalibai sama da dari da aka sace su tare, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana bakin cikin gaza ceto ‘yammatan tare da sake yin alkawarin ceto su.
Sai dai kungiyar fafatukar ceto 'yammatan da taken Bring Back Our Girls, tace gwamnatin tana ci gaba da kura kurai dangane da wannan batun, musamman ta fannin hulda da iyayen yammatan.
Saurari shirin domin karin bayani
Facebook Forum