Wani mutum da ake kyautata zaton dan kungiyar al-Qaida ne ya rasu ‘yan kwanaki kafin a fara yi mashi shari’a a birnin NY, sabili da harin boma boman da aka kai kan ofishin jakadancin Amurka a Afrika cikin shekara ta dubu da dari tara da casa’in da takwas.
Lauyan Abu Anas al-Libi yace mutumin da yake karewa yana fama da ciwon hanta da kuma cutar sankaran hanta, ya rasu jiya jumma’a a wani asibiti dake NY.
Dama za a fara sauraron karar da aka shigar kan Libi da Khalid al-Fawwaz, wani dan kasar Saudiya ranar goma sha biyu ga wannan watan na Janairu, sabili da hare haren da aka kai a Kenya da Tanzaniya da suka yi sanadin mutuwar mutane dari biyu.
Bernard Kleinman lauyan Libi yace, jikin mutumin da yake karewan ya yi tsanani cikin wata guda da ya shige.
Libi da Fawwaz sun musanta aikata laifukan hada baki da ake tuhumarsu a kai.
Jami’an tsaron Amurka na musamman ne suka kamo Libi a Tripoli a watan Oktoba shekara ta dubu biyu da goma sha uku. Yana cikin jerin wadanda hukumar binciken ta Amurka FBI take nema ruwa a jallo