A rahoton da wakilin Muryar Amurka(VOA) Ladan Ibrahim Ayawa ya aikowa sashen Hausa na cewa , hakan ba shine karon farko da hukumar “Railway” ta Nigeria ta fara wnanan shirin ban a gyaran ayyukan zirga-zirgar jiragen kasa.
A watan Maris, wato watan Ukun farkon wannan shekarar, jirgin kasa dauke da fasinja ya tashi daga tashar Ikko zuwa Ibadan, shalkwatar jihar Oyon Nigeria, duka a cikin shirin maido da zirga-zirgar daki-daki. Ran Alhamis ake shirin gudanar da mataki na biyu, sannan makatki na uku sine wanda zai taso daga Ikko zuwa Kano. Idan ba’a manta ba, tun watan Satumban day a gabata ne Gwamnatin Tarayyar Nigeria ta sayo sabbin kan tukwanen jiragen kasa guda 25 kuma an rarrabasu duk zuwa sauran tashoshin jiragen kasa a Nigeria.