Kanal Hassan Mohammed, babban jami’in sojin Nigeria dake aikin maido da zaman lafiya a Maiduguri, jihar Borno Arewa maso gabashin Nigeria yace jami’an tsaron Nigeria na ci gaba da binciken gida-gida a Maiduguri jihar Borno domin gano muggan makaman da ‘yan tsagera suka boye da niyyar kai hare-haren ta’addanci a lokacin bikin sallar layya.
A tattaunawar da yayi da manema labarai, kanal hasan Mohammed yace makasudin gudanar da binciken gida-gidan da soja keyi yanzu shine a hana samun nasarar shirin ‘yan kungiyar Boko Haram na tada zaune tsaye. Yace an dauki karfafan matakan tsaro bayan wa’adin da aka bayar na mika makamai yak are. Ya zuwa yanzu dai yace an kama mutane masu yawa da ake zargin boye makamaki a gidajensu, an kuma kama makamai masu tarin yawa.