Kungiyar Boko Haram ta kasar Najeriya ta dauki alhakin kashe wani dan jaridar daukan hoto mai aiki a talbijin din jahar Borno.
Wani kakakin kungiyar Boko Haram ya fada a yau talata cewa kungiyar ce ta kashe Zakariyya Isa saboda ya na yiwa hukumar tsaron kasar Najeriya leken asiri a kan su. Kakakin ya ce bayanan leken asirin da Zakariyya Isa ya tattara sun taimaka wajen kama dimbin 'yan kungiyar Boko Haram.
Zakariyya Isa ya rasu ranar Lahadi a garin Maiduguri bayan harbin da aka yi mi shi ranar asabar da daddare daga fitar shi daga wani wani Masallaci. Babu wata shaidar da ta nuna cewa Zakariyya Isa dan leken asiri ne.
A watan jiya na Satumba kungiyar Boko Haram ta yi barazanar cewa za ta fara kai hari kan 'yan jaridan da ba sa yi mata adalci a cikin labaran da suke bayarwa. A cikin sanarwar da ta yi Talatar nan kungiyar ta ce ba za ta yi shayin kashe duk wanda ya cuta ma ta ba.
Boko Haram mai adawa da ilimin zamani irin na kasashen Turawa, ta ce gwagwarmayar da ta ke yi ta neman kafa wani yanki ne mai 'yancin kai a Najeriya, wanda za ta tafiyar da mulkin shi bisa tsarin Shari'ar Islama.