A Jamhuriyar Nijar wata gobara ta barke a sansanin ‘yan gudun hijira da ke garin Toumour na yankin Diffa, lamarin da ya yi sandiyar mutuwar mutane 2 tare da lakume daruruwan gidaje.
Lamarin ya faru da misalin karfe 12 na ranar yau laraba, inda gobarar ta ci karfin mutanen da ke kokarin kashewa, sakamakon iskar dake kadawa a lokacin, abin da ya janyo konewar daruruwan gidajen ‘yan gudun hijira har ma da asarar rayukan mutane biyu.
Amadou wanda lamarin ya auku a gabansa ya shaidawa wakilin muryar Amurka ta wayar tarho cewa wutar ta lakume gidajen fiye da dari uku.
Magajin garin Toumour Maire Issane ya ce a halin yanzu ana shirin gudanar da bincike domin tantance mafarinta da irin barnar da ta haddasa.
‘Yan gudun hijira daga Najeriya da ‘yan gudun hijira a cikin Nijar sama da 200,000 ne ke samun mafaka shekara da shekaru a yankin Diffa, sakamakon rikicin Boko Haram, yayin da wasu daga cikinsu suka matsu a mayar da su garuruwansu na asali, wasunsu kuma na ganin lokaci bai yi ba ganin yadda ake ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci a yankunan da suka fito.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum