Ya zuwa yanzu yawan mutanen da suka mutu sakamakon girgizar kasa mai karfin kaso 7.8 a Kathmandu ta kasar Nepal ya karu zuwa dubu biyu da dari biyu, sannan jama'a da dama sun jikkata.
Girgizar kasar ta zubar da gine-gine da katangun jama’a wanda hakan ya koro jama’a kan tituna a firgice. Majiyoyi sun fadawa Muryar Amurka cewa girgizar kasar ta yi barna sosai ciki harda gine ginen tarihi irin su ginin Kathmandu.
Masu aikin agaji suna ci gaba da kai dauki ga wadanda abin ya rutsa da su. Shima babban ginin nan na tarihi a karni na 19 mai suna Ginin Kathmandu ya zube inda ake zaton ya murkushe jama’a da dama.