An gudanar da wani taron masu ruwa da tsaki a Umuahia, babban birnin jihar Abia, inda aka hada manyan mutane da suka hada da ‘yan siyasa, sarakuna, ‘yan kasuwa, malaman addinai da dai sauransu.
Taron, wanda ya hada al’umma baki daya babu banbancin siyasa ko akida da kabilanci. A taron an maida hankali ne akan muhimancin zaman lafiya a cikin al’umma, inda aka kara jan hankalin mutane da su ji tsoron Allah wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullun. Zanga-zangar kawo karshen rundunar ‘yan sanda ta SARS ta sa kasar baki daya shiga cikin wani hali.
A cewar Alh. Yaro Danladi, shugaban majalisar sarakunan Hausawa yanki kudu maso gabas, taron ya maida hankali ne akan fadakar da al’umma, inda gwamnan jihar da kansa ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda aka yi wa ‘yan arewa mazauna jihar. Mun bayyana kukanmu, inda kuma gwamnan ya sha alwashin kawo karshen irin yadda ake musguna ma wasu.
Gwamnan yayi tattaki zuwa birnin Abba don ganewa kansa irin barnar da aka yi wa Hausawa da nufin kawo karshen irin wannan aika-aikar. A bangare daya kuwa, Mal. Tukur Garba, ya na ganin cewar ya kamata mutane su mai da hankali, su daina barnata dukiyoyin al’umma da sace-sace, dan yin hakan ba hanyar yin arziki ba ce.
Ya ce babu wanda zai yi arziki da dukiyar sata, don haka mutane su maida hankali wajen kawo karshen rashin jituwa a tsakaninsu musamman a zamantakewar yau da kullun.
Ga rahoton Alphonsos Okoroigwe a cikin sauti:
Facebook Forum