Babban darektan ma’aikatar kiwon lafiyar Ghana, Dakta Patrick Kumah Aboagye ya bayyana irin halin da ake ciki game da allurar rigakafin covid 19 a garin Juase na yankin gabashin kasar, yana mai cewa Gwamnati ta yi farin ciki game da yadda aka fito sosai a farkon yin allurar, tana kuma kira ga kowa ya shiga shirin ta yadda za a kara samun nasarar aikin bada rigakafin.
Ya ce wannan adadin shi ne bayanai da suka tattara daga yankuna bakwai da suka hada da yankin Ashanti wanda ke da kashi uku cikin dari na adadin wadanda suka yi allurar da kuma aka musu rajista.
Da yake bayyana rukunin mutanen da aka fi ba su muhimmanci a wannan aiki, Dakta Patrick Aboagye ya ce, “Mun fi maida hankali kan ma’aikatan kiwon lafiya da tsofaffi masu shekaru sittin, sai kuma wadanda ke da wasu cututuka kamar na hawan jini da cutar sikari da kuma wadanda ba su da lafiya amma ba marasa galihu ne ba da kuma ma’aikatan tsaro.
“Sai dai ni a gani na, wadanda suka fi sa kai sosai cikin aikin alurar ne masu shekaru sittin ko fiye da haka. Sune keda mutane 51,000 da suka karbi rigakafin , ma’aikatan kiwon lafiya dubu 27 da masu fama da lalurori dubu 51 suka karbi rigakafin.
Dakta Patrick Aboagye ya kuma bada sanarwa cewa ana sa ran shigowa da karin allurar rigakafin milliyan biyu kafin karshen watan mayu.
Zamu kuma yi aiki a kan fuska ta biyu na bada allurar Covid 19 daga yanzu zuwa karshen watan mayu kana muna sa ran samun maganin milliyan biyu bisa ga irin yarjejeniya da muka kulla.
A karshe za a bude wani shafin yanar gizo da za a rika rajistar masu neman karbar allurar, haka zalika za a kuma bude cibiyoyin gudanar da aikin bada rigakafin.
Ga Ridwan Muktar Abbas da rahoto daga birnin Accra: