Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gavi Ya Tsawaita Kwatiraginsa Da Barcelona Zuwa 2030


Gavi da Shugaban kungiyar kwallon kafar Barcelona
Gavi da Shugaban kungiyar kwallon kafar Barcelona

Dan wasan da ya taka wa kulub din leda har sau 27 ya yi fama da rauni mai tsanani a gwiwarsa yayin da ya ke bugawa kasar Sifaniya wasa a watan Nuwamban 2023, inda ya rasa damar taka rawa a nasarar da kasarsa ta samu a gasar zakarun Turai ta 2024.

Dan wasan tsakiyar Barcelona Pablo Paez Gavira, da aka fi sani da Gavi, ya tsawaita kwantiraginsa da zakarun gasar La Liga Barcelona zuwa watan Yunin 2030, kamar yadda kulub din ya shelanta a yau Juma’a.

Yau shekaru 10 kenan da zuwan Gavi Barcelona, inda ya fara buga wa kungiyar wasa a watan Agustan 2021, lokacin yana da shekaru 17.

Sai dai dan wasan da ya taka wa kulub din leda har sau 27 ya yi fama da rauni mai tsanani a gwiwarsa yayin da ya ke bugawa kasar Sifaniya wasa a watan Nuwamban 2023, inda ya rasa damar taka rawa a nasarar da kasarsa ta samu a gasar zakarun Turai ta 2024.

“Kungiyar Barcelona da Gavi sun cimma yarjejeniyar sabunta kwatiragi, kuma a shirye yake ya ci gaba da zama a kulub din har zuwa ranar 30 ga watan Yunin 2030,” a cewar kulub din.

.Ya ciwa kulub din kwallaye 9 sai dai ya bata kusan tsawon shekara guda kafin ya dawo a watan Oktoban 2024.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG