Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Man City Za Ta Kara Da Real Madrid A Wasan Tantancewa Na Gasar Zakarun Turai


Gasar Champions League
Gasar Champions League

City, wacce ta sha da kyar bayan da ta karkare a mataki na 22 a zagayen lig na kakar farko ta sabon salon gasar fitattun kungiyoyin kwallon kafar Turai, za ta kasance a gidanta a zagayen farko kafin ta zarce zuwa Sifaniya domin karawa ta 2.

Masu rike da kambun zakarun Turai na yanzu Real Madrid zasu kara da zakarun gasar na 2023 Manchester City a zagayen wasannin tantance zakaran gasar na kakar bana, sakamakon fitar da jadawalin da aka yi a yau Juma’a.

Wannan ne karo na 4 da ake hada bangarorin 2, inda Real Madrid ta samu galaba a bugun finareti a zagayen kwata fainal.

City, wacce ta sha da kyar bayan da ta karkare a mataki na 22 a zagayen lig na kakar farko ta sabon salon gasar fitattun kungiyoyin kwallon kafar Turai, za ta kasance a gidanta a zagayen farko kafin ta zarce zuwa Sifaniya domin karawa ta 2.

A wani labarin kuma, Celtic za ta kara da kungiyar da ta lashe gasar zakarun Turai har sau 6, Bayern Munich, bayan da zakarun na yankin Scotland suka samu nasarar kaiwa zagayen kifa daya kwale a karon farko cikin shekaru 12.

Kungiyar Paris Saint-Germain za ta baiwa brest mamakin a karawar kungiyoyin kwallon kafar Faransa zalla, yayin da Juventus za ta kara da PSV Eindhoven sannan Feyenoord za ta hadu da AC Milan a wasannin 2 tsakanin tsaffin zakarun nahiyar Turan guda 2.

Za’a buga wasannin tantancewar ne a wata mai zuwa, inda kungiyoyi 8 da suka samu nasara zasu tsallaka zuwa zagayen ‘yan 16 tare da wasu kungiyoyin 8.

Ga yadda sauran jadawalin ƙungiyoyin ya kasance:

  • Brest v Paris St-Germain
  • Club Brugge v Atalanta
  • Manchester City v Real Madrid
  • Juventus v PSV
  • AS Monaco v Benfica
  • Sporting v Borussia Dortmund
  • Celtic v Bayern Munich
  • Feyenoord v AC Milan

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG