Dan wasan Real Madrd Kylian Mbappe ya ce sauya tunaninsa da ya yi ne ya sa tauraronsa ya fara haskawa a kungiyar.
“Na kan yawan yin tunani da yawa akan komai, kan yadda zan tafiyar da al’amura, yadda zan nuna kai na a filin wasa...... Idan kuma kana yawan tunani, hakan ba zai bari ka yi kwallo da kyau ba.” In ji Mbappe.
Mbappe ya yi ta taga-taga a farkon zuwansa kungiyar ta Madrid kafin daga bisani ya samu daidaito a yadda yake taka leda.
Amma a ‘yan kwanakin nan ya farfado a taka ledar da yake yi inda tauraronsa yake haskawa.
Mbappe ya taka muhimmiyar rawa a karawar da Madrid ta ci Las Palmas da ci 4-1 a gasar La Liga a ranar Lahadi.
Dan wasan na da kwallaye hudu a wasanni hudu da Madrid ta buga a baya-bayan nan.
Dandalin Mu Tattauna