Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Minista Boris Johnson Yana Samun Sauki - Jami'an Birtaniyya


A yau Laraba wani jami’in kasar Birtaniya ya ce Firayim Minista Boris Johnson yana samun sauki bayan da ya shafe kwanaki biyu a sashen da ake ba marasa lafiya kula ta musamman a asibitin Landon inda yake jinyar cutar coronavirus.

Karamin Ministan Lafiya na kasar Edward Argar, ya ce Johnson yana cikin kyakkyawan yanayi da koshin lafiya.

Tun a ranar Lahadi 5 ga watan Afirilu ne aka kwantar da Firayim Ministan a asibiti bayan da jikinsa yayi zafi a lokacin da ya killace kansa, biyo bayan gwada shi da aka yi aka kuma same shi da cutar coronavirus.

Birtaniya, wacce take karkashin dokar hana zirga-zirga kusan makonnin biyu, tana da kusan mutane 56,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus, wasu su 6,100 kuma sun mutu.

Koriya ta Kudu bata bi sahun wasu kasashe da dama ba na kafa matakai masu tsauri na zama a gida, amma ta yi nasara sosai wajen rage adadin mutanen dake ke kamuwa da cutar tare da yin kira akan jama'a su rinka yin nesa-nesa da juna da kuma rufe makarantu.

Gwamnatin kasar ta sanar da cewa an sami karin mutane 53 da suka kamu da cutar a yau Laraba.

Akwai fargabar yiwuwar samun karin adadin wadanda zasu kamu da cutar a Seol babban birnin kasar, kana a yau Laraba magajin garin birnin ya sanar da rufe gidajen barasa da wuraren shakatawa na dare.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG