Jami'an kiwon lafiya a China sun ce ba a sami mutuwa ko daya ba sanadiyar cutar coronavirus a cikin sa'o'i 24, wannan shine rahoto irinsa na farko tun daga watan Janairu.
A yau Talata hukumar lafiya ta kasar ta ce sabbin alkaluman mutane 32 ne kadai aka samu da suka kamu da cutar ta COVID-19 kuma dukkansu sun dawo ne daga kasashen ketare.
Raguwar adadin mace-mace da kuma sabbin masu kamuwa da cutar na zuwa ne a yayin da lardin Hubei ke shirin sassauta matakan hana fita a birnin Wuhan inda cutar ta fara barkewa a bara.
Kasar China ta sami adadin mutane 80,000 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus tun lokacin da cutar ta barke, gami da mutuwar mutane 3,331. Hukumar kiwon lafiyar ta ce an killace mutane 1,033 dake da cutar amma basu nuna alamun rashin lafiya ba, ko da yake zasu iya yada wa wasu cutar.
Facebook Forum