Wani hoto da fadar shugaban Najeriya ta fitar ya nuna Firai Ministan Habasha Abiy Ahmed yana tuka shugaba Muhammdu Buhari a cikin wata bakar mota a lokacin da ya isa kasar.
“Firai Ministan Ethiopia, mai girma Abiy Ahmed yana tuka Shugaba Muhammadu Buhari suna fita a filin tashin jirage yayin bayan da ya isa Addis Ababa.” Mai bai wa Buhari shawara kan sha’anin kafafen sada zumunta na zamani Bashir Ahmed ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A ranar Lahadi Buhari ya isa Addis Ababa, babban birnin kasar ta Habasa don halartar bikin rantsar da Firai Minista Ahmed a wa’adi na biyu.
Baya ga wannan hoto, Kakakin Buhari Femi Adesina ya wallafu wasu da suka nuna yadda aka yi wa Buhari tarba ta girmamawa a filin tashin jiragen na Addis Ababa yayin da ya sauka.
Bayan haka ne kuma Firai Minista Ahmed ya dauki Buhari a mota suka fice a filin jirgin.
Wata sanarwa da Adesina ya fitar a ranar Asabar ta ce Buhari na daga cikin manyan bakin da za su yi jawabi a wajen bikin rantsar da Ahmed, wanda zai yi wani wa’adin shekara shida.
Daga cikin wadanda suka rufa masa baya a cewar sanarwar wacce Kakakinsa Femi Adesina ya fitar, akwai “Ministan harkokin wajen Geoffrey Onyeama da Babban Darektan hukumar tattara bayanan sirri Ambasada Ahmed Rufai Abubakar.
Firai Ministan Ahmed ya samu nasarar wani sabon wa’adin shekara biyar ne bayan da jam’iyyarsa ta Prosperity Party mai mulki ta samu nasara a zaben ‘yan majalisar da aka yi a ranar 21 ga watan Yuni.
Tun bayan samun nasarar, shugaban Najeriya ya taya Ahmed murnar lashe zaben inda ya tabbatarwa da kasar cewa “Najeriya za ta ci gaba da tallafa mata da sauren kasashen nahiyar wajen hadin kasa da zaman lafiya a yankunansu.”