Kwamishinan 'Yan sandan jihar,Jeremiah Undie ya bayyana a wani taron manema labarai cewa, sun kwato bindigogi 171, da harsasu mai jigida 795 da wasu harsasu 131.
"Bari na yi amfani da wannan damar domin karfafa gwiwar sauran jama'ar da ba su gabatar da makamansu ba, da su yi hanzarin yin hakan kafin cikar wa'adin mayar da makamai bisa radin kai wato karshen watan Afrilu ya wuce," inji kwamishinan.
Haka kuma an bayyana wasu bata-garin da suka sace motoci 11, da masu satar babura, da sojin gona da har wasu da ake zargin sun aikata laifin kisa.
"Wallahi na kashe wani yaro bafullatani ne da shanunsa suka hau kan wani tarin doya, shine na zo na koreshi ko na kamashi amma sai ya tsere. Sai harbeshi yayin da ya ke guduwa." inji wani da ake sameshi da laifin kisa
Wani daga cikin wadanda aka samu da laifin sace babura cewa yayi:
"Gaskiya na shiga wani hali ne, dan uwana ba shi da lafiya, an yi kokarin asibiti amma ba ni da kudi kuma ni ne babba."
Wannan matashin ya kuma shawarci sauran matasa da su daure su nemi sana'a domin gujewa fadawa halin bata-gari.
Saurari cikakken rohoton Zainab Babaji.
Facebook Forum