Manjo Janar David Ahmadu,babban hafsan dake kula da aikace aikace a hedkwatar sojojin Najeriya shi, ya bayyana taron sojojin na kasa da kasa tare da sojojin Amurka dake nahiyar Afirka ko AFRICOM.
Yau za’a fara taron wanda zai ba manyan hafsoshin sojojin Afirka damar yin nazari akan harkokin tsaro a kasashensu tare da samun hanyoyin tunkarar kalubalen a nahiyar.
Duk shekara Amurka ta hannun AFRICOM tana shirya taron a Afirka da kasashen dake kawance da ita domin musayar bayanai akan ta’addanci da kuma yadda za’a fuskanci ayyukan ta’addanci tsakanin kasa da kasa, da dakile yaduwar kananan makamai da wasu aika aika.
Inji Manjo Janar David Ahmadu ya zuwa yanzu duk manyan hafsoshin kasashen Afirka sun isa Abuja. Taron shi ne mafi girma a tarukan sojojin Afirka da na kasashen Turai da ma Amurka.
Zasu tattauna sosai kan rushewar kungiyar ISIS A Syria da Iraqi da irin abun da ta haifar a nahiyar Afirka wajen tabarbarewar zaman lafiya da tsaro.
Yayin taron bataliya ta 176 dake tsaron Fadar Aso Rock ta shugaban kasa zata yi atisayi na musamman, a matsayin wani yunkurin gwada karfi.
Dangane da mahimmancin taron Malam Kabiru Adamu, wani masanin harkokin tsaro, a cewarsa shugaban Amurka ya bukaci a yaki ta’addanci a koina amma kuma baabun ne da kasa daya zata yi ita kadai ba, dalili ke nan da yake bukatar a hada karfi da karfe wajen kawar da wannan bala’in. Akwai kuma tsoron da Amurka ke dashi na cewa China tana kara karfi a Afirka saboda haka a wurin taron Amurka zata so ta cusa wa kasashen ra’ayinta.
Hassan Maina Kaina nada karin bayani
Facebook Forum