A farkon makon nan, mai magana da yawun rundunan sojin Najeriya Laftanal TG Iortyom, mukaddashin kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, dake aikin tabbatar da zaman lafiya ta bada sanarwar bullowar wata kungiya mai suna “Hakika”.
Sanarwar ta bayyana cewar kungiyar ta bullo ne a yankin kananan hukumomin Yola ta Kudu a jihar Adamawa da Toto na jihar Nasarawa.
‘Yan kungiyar karkashin jagorancin wani mai suna Yahaya Ibrahim sun bullo da wasu akidu da suka hada da daina yin sallah biyar (5) a rana, daina yin azumi da daurewa zina gindi.
Wani Malami a Ngurore, wanda baya son a ambaci sunan sa, inda yan kungiyar suka zauna kwanaki, yace yanzu babu burbudinsu a garin kamar yadda ake yayatawa. Hakan ya faru ne bayan an ankarar da jami’an tsaro. Y ace sun san basa kan akidar kwarai dalili ke nan suka tashi tsaye suka tabbatar sun fice daga garin. Y ace sun lura basa yin sallah. Suna shan giya tare da yin muamala da matan banza.
Yanzu haka dai hukumomin tsaro a jihar Adamawa sun baza jami’ansu don bincike tare da yiwa jama’a gargadin su sanar da hukuma da zara sun ji duriyarsu.
SP Othman Abubakar kakakin rundunan yan sandan jihar y ace suna sane da lamarin suna kuma ci gaba da bincike. Yace sun baza jami’an tsaronsu na farin kaya su shiga jama’a su gano masu hakikanin gaskiyar lamarin domin su magancesu cikin hanzari. Y ace rashin bin Kadin abun da suke koyaswa ya sa wasu matasa suna bijirewa.
A shekarun baya, an taba samun bullar wasu yan wata kungiyar a kauyen Mamukan ,lamarin da ya kai hukumomin tsaro dirar mikiya da kuma rusa wurin ibadarsu.
A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz
Facebook Forum