Wata kungiyar matasa masu basirar kirkiro da manhajar na’aurar kwamfuta da kuma kwararru a fannin fasaha sun gano cewa, farashin magunguna a Najeriya yana iya ruba madaidaicin farashi na kasashen duniya har sau tara.
Kamfanonin sarrafa magunguna a Najeriya suna jin komadar tattalin arziki a jikinsu. Farashin magunguna a shagunansu ya tashi da kashi arba’in cikin dari cikin watanni shida da suka shige. Funmi Bola Omotayo, wata mai ilimin sarrafa magunguna ta bayyana cewa, tana tausayawa abokan cikinikinta.
Tace zaka iya cewa, iya sayen magunguna shine rai. Cuta ba zata iya sanin ko zaka iya sayen magani ba ko babu. Tace abokan cinikinta kadan ne suke da inshorar lafiya da zata sassauta masu farashin magunguna. Galibin magungunan da ake sayarwa a Najeriya ana shigo da shi ne daga kasashen ketare.
Masu sharhi kan kula da lafiyar al’umma sun ce kasa da kashi talatin cikin dari na magungunan da ake sayarwa a Najeriya ne ake sarrafawa a kasar.
Yace zan iya cewa, magani yana tsada ne sabili da komadar tattalin arziki da ake fama da ita a kasar.
Sai dai tun kafin faduwar tattalin arzikin Najeriya bana, maguguna suke tsada a Najeriya.
Binciken da hukumar lafiya ta duniya da kuma gwamnatin tarayyar Najeriya suka gudanar a shekara ta 2002 da 2010 ya nuna cewa, magunguna a Najeriya ya yi ninkin ba-ninki kan madaidaicin farashin magunguna na kasashen duniya. Binciken da aka gudanar a shekara ta 2004 ya nuna cewa, farashin da dillalai ko kuma masu saida magunguna suke saidawa ya ruba abin da kamfanonin sarrafa magunguna suke saida shi da kimanin kashi dari tara cikin dari.
Wannan yasa wata kungiyar kwararru a fannin na’urar komputa kirkiro da wata manhaja da zata taimaki masu amfani da ita wajen sanin farashin magunguna.