A jiya Laraba ne Majalisar Ministocin Najeriya ta amince da wannan tsari, a wani mataki na karfafa aikin da gwamnati ke yi da ayyukan rashawa.
Kwamarad Nura Iro, yace idan har da gaske ake a yaki da rashawa, kamata yayi a baiwa duk wani mutum da ya bada bayanai tukwicinsa koda kuwa bayanan basu kai ga karbo kudin ba.
Kasancewar akwai doka da ta yanke wasu adadin kudi da shugaban kasa zai iya kashewa ba tare da ya nemi izini daga Majalisa ba. A ganin Barista Tahir Mohammad, dole a dubi kudin tukwicin da za a bayar ko ya haura adadin kudin da dokar ‘kasa ta yanke ayi amfani da shi ba tare da neman izinin Majalisa ba, idan kudin ya haura to tabbas za a iya samun tsaiko ga wannan batu.
A cewar Barista Sanusi Umar, yaki da cin hanci da rashawa alhakine da ya rataya a wuyan dukkanin ‘yan Najeriya, ko da tukwici ko babu. Ya kuma kara da cewa kamata yayi a yi dokar da zata ke tsorata mutane, kamar idan mutum ya ga ana wata almundahana kuma baiyi magana ba to abin zai shafe shi.
Domin karin bayani ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.