A wani biki da aka nuna ta talabijin, Damiba ya sha rantsuwar kama aiki a gaban manyan jami’an shari’ar Burkina Faso, don kare kundin tsarin mulki da mutunta shi, da kuma bin dokokin kasar, da ma wasu muhimman dokoki da gwamnatin sojan za ta amince da su.
'Yan jarida, amma ban da wakilan kasashen waje, sun halarci bikin a wani karamin daki a ofisoshin Majalisar Tsarin Mulkin kasar.
A ranar 24 ga watan Janairu, Damiba, mai shekaru 41, ya jagoranci sojoji wajen hambarar da Kabore biyo bayan bacin ran da jama’ar kasar suka nuna akan yadda ya takali mummunan tashin hankalin ‘yan ta’adda.
A makon da ya gabata ne Majalisar Tsarin Mulkin kasar ta tabbatar da cewa Damiba shi ne shugaban kasa, kuma babban kwamandan sojojin kasar.
Matakin ya tabbatar da sanarwar da gwamnatin sojan ta fidda ranar 31 ga watan Janairu cewa, za a ba Damiba wadannan mukaman tsawon lokacin gwamnatin rikon kwaryar, kuma zai samu mataimakan shugaban kasa biyu.
Burkina Faso dai na daya daga cikin kasashen da suka fi fama da talauci a duniya kuma ta na daga cikin kasashen Afirka da ke fama da rikice-rikice.
Haka kuma kasar da ke yammacin Afrika, ta sha fuskantar juyin mulki tun bayan samun 'yanci daga Faransa a shekarar 1960.