Sakamakon farko ya nuna cewa, Salma Bint Hizab Al- Otiebi, ta zamanto mace ta farko da ta lashe zaben, inda ta doke maza bakwai da wasu mata biyu da suma suka tsaya neman kujerar Madrakah, gundmuar da ke da tazarar kilomita 150 da arewacin Makkah.
Shafukan yada labarai na gwamnati da saurarn kafafan yada labarai masu zaman kansu sun bayyana cewa akalla mata 17 ne suka yi nasara a wannan zabe, sai dai babu wani sakamako na karshe da aka fitar a hukumance.
Akalla mata 900 ne suka tsaya takarar neman mukamai dubu biyu, duk da irin kalubalan da suka fuskanta wajen neman takarar da kuma yin rajista, kamar yadda kungiyar Human Rights Watch mai kare hakkin bil adama ta bayyana.
Kungiyar ta Human Rights Watch ta kara da cewa nisan rumfunan zabe da inda matan suke, da kuma rashin katin sheda da mafi yawan matan ba su dashi, na daga cikin ababan da suka janyo cikas wajen gudanar da zabukan.