Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fadar Shugaban Najeriya Ta Bayyana Halin Da Buhari Ke Ciki


Shugaban Najeriya Buhari a lokacin da ya ke karbar bakuncin wasu gwamnonin jam'iyarsa ta APC da wasu shugabanninta, ranar 23 ga watan Yuli, Hoton Aso Rock, Najeriya
Shugaban Najeriya Buhari a lokacin da ya ke karbar bakuncin wasu gwamnonin jam'iyarsa ta APC da wasu shugabanninta, ranar 23 ga watan Yuli, Hoton Aso Rock, Najeriya

Wata ziyara da wasu gwamnoni da shugabannin jam'iyar APC a Najeriya suka kai wa shugaba Muhammadu Buhari,a gidan da yake jinya a birnin London a Birtaniya, ta kara fito da halin da shugaban ke ciki wanda ya kwashe wani tsawon lokaci yana jinya a Birtaniya.

Fadar shugaban kasar Najeriya ta Aso Rock, ta fitar da wata sanarwa kan halin da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke ciki, bayan da wasu gwamnoni da shugabannin jam’iyar APC mai mulki suka ziyarce shi a gidan da yake jinya a birnin London.

Wata sanarwa dauke da sa hannun mai bai wa shugaban shawara kan harkar yada labarai, Femi Adesina, wacce aka wa take da “Yadda Mu Ka Ga Buhari- A Fadin Gwamna Okorocha.” Ta nuna cewa shugaban na samun sauki sosai,

Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha na daya daga cikin gwamnonin da suka ziyarci Buhari a jiya Lahadi, shi ne kuma ya fadi halin da Buhari ke ciki a cewar sanarwa wacce aka rubuta ta da harshen ingilishi.

“Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, ya ce shugaba Muhammadu Buhari na cikin koshin lafiya – kuma yana nan da wasansa na barkwanci.” Sanarwar ta bayyana."

Shugaba Buhari wanda ya nuna farin cikinsa da ziyarar gwamnonin da shugabannin jam’iyar, ya kwashe sa’a guda yana tattaunawa da su kuma ga dukkan alamu yana sane da duk abinda ke faruwa a gida (Najeriya), a cewar sanarwar.

Shugaba Buhari ya kuma tambayi ministan kula da sufuri, Rotimi Amaechi (wanda shi ma yana cikin tawagar) kan halin da fannin sufurin jirgin kasa kasar ke ciki.

A lokacin da aka tambayi shugaba Buhari kan irin kalamai mara dadi da ake fada a kansa, sanarwar ta nuna cewa, “shugaban sai ya yi dariya, ya kuma kwatanta kalaman akan wadanda aka dasa su akan karerayi. Kuma gwamna Okorocha ya bayyana cewa babu wata da ta nuna cewa Buhari ya damu da maganganun da ake yi akansa – maimakon haka sai ya ce yana mika sakon gaisuwarsa ga ‘Yan Najeriya.”

“Kada ‘Yan Najeriya su damu ko kadan, shugaban Buhari zai dawo nan ba da jimawa ba, da zaran likitocinsa suka amince.” Sanarwar ta kara fada.

“Da wannan ziyara da muka kai yau (Lahadi) a London, karyar masu yayata jita-jita ta kare, saboda ‘yan Najeriya ba za su yadda da jita-jitar da suke yadawa ba, kuma duk wadanda suke bi-biyan labaran karya, gara su yi wani abu daban da lokacinsu.” In ji Okorocha, kamar yadda sanarwa ta bayyana.

Baya ga gwamna Okorocha na jihar Imo da minsitan sufuri Amaechi da ke cikin tawagar, har ila yau akwai gwamnan jihar Nasarawa Umaru Tanko Al-Makura, da Nasiru El – Rufai na Kaduna da Yahaya Bello na Kogi, da kuma shugaban jam’iyar ta APC na kasa, Cif John Oyegun.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG