Wannan bukata ta bayyana ne a wata sanarwa da kamfanin mai na kasa ya rabawa manema labarai a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.
Jakadar kungiyar Turai a Najeriya Samuela Isopi ita ce ta jagoranci sauran jakadun kasar Spain da Italiya,da Portugal da kasar Faransa a lokacin da suka kai ziyarar ban girma ga kamfanin Man Fetur na Najeriya.
Isopi ta ce Najeriya ce kasa ta hudu da ke samar da iskar gas zuwa Turai, inda ta ce Najeriya tana fitar da kashi 40 cikin 100 na Gas zuwa kasashen Turai a halin yanzu.
Karamin Ministan Man Fetur na kasa Timipre Sylva ya yaba da wannan mataki da kasahen Turai suka dauka inda ya ce Najeriya a shirye ta ke ta shiga yarjejeniyar kara yawan iskar gas ga kasashen na Turai.
Timipre Sylva ya bayana cewa tuni har an fara shinfida bututan da za su kai iskar gas zuwa kashen Turai ta kasar Aljeriya.
Sylva ya ce akwai kuma shimfida bututu ta kasar Morocco, dukan wadannan ayyuka an riga an fara su gadangadan, kuma Najeriya a shirye ta ke ta zama abokiyar kasuwanci ga kasashen Turai.
Da ya ke tofa albarkacin bakin sa a game da wannan bukata, kwararre a fannin Gas da Man Fetur Mohammed Sale Hassan ya kalli wannan neman karin iskar gas daga Najeriya zuwa kasahen Turai ta fannin rashin karfin tattalin arzikin kasar ne
Shi ma masanin tattalin arziki Abubakar Ali ya yi karin haske akan wannan bukata da ya ke ganin tarihi ne zai maimaita kansa kuma zai habbaka fannin kasuwanci a tsakanin kasashen.
Sanarwar ta ce kungiyar Tarayyar Turai ta bayana bukatar kara yawan iskar gas da ta ke saye daga Najeriya ne, biyo bayan yakin da a ke yi tsakanin Rasha da Ukraine domin cike gurbin gas din da kungiyar Turai ke saye daga kasar Rasha.
Saurari rahoto cikin sauti daga Medina Dauda: