Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duk Da Kara Wa’adin Canja Tsoffin Kudi ‘Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Nuna Fargaba


Layi a bankunana Najeriya
Layi a bankunana Najeriya

A yau 10 ga watan Fabarairu ne babban bankin Najeriya CBN ta bayyana cewa za a daina amfani da tsoffin takardun kudaden da aka canza na Naira 200, 500 da 1000 lamarin da ya haifar da fargaba a zukatan mutane da dama a kasar ganin irin cunkoso da ake fuskanta a wasu bankunan kasar.

ABUJA, NIGERIA - Kazalika a yau daruruwan kwastamomi sun taru a harabar bankin Zenith dake unguwar Asokoro a babban birnin tarayya Abuja, inda suke kokarin shiga bankin don samun biyan bukata.

Masu Layin canja kudi a Najeriya
Masu Layin canja kudi a Najeriya

Sai dai wannan lamari na zuwa ne adaidai lokacin da gwamnatin Najeriya ta ce za ta mutunta umarnin da Kotun Kolin kasar ta bayar a kan karar da wasu gwamnonin Jihohi uku suka shigar inda kotun ta dakatar da aiwatar da wa'adin daina amfani da tsofaffin takardun kudi har zuwa ranar 15 ga watan nan da ake ciki inda za a yi zaman sauraron hukunci da za a yanke.

Tun da fari dai wasu ‘yan Najeriya sun nuna goyon bayansu ga matakin gwamnatin kasar da CBN na sanya wa’adin dakatar da amfani da tsoffin kudin da aka canja. Muhammad Saleh Hassan, shugaban kungiyar One Nigeria na daya daga cikin ‘yan kasar da suka nuna goyon bayansu ga matakin.

Shi ko ana shi bangaren Mastura Ashir Sheriff shugaban kwamitin Amintattu na Gamayyar Kungiyoyin Arewancin Najeriya na ganin wannan hukunci da kotun kolin kasar ta yanke ya yi daidai, duba da halin da ‘yan kasar suka tsinci kansu a ciki, ya kuma kara da cewa tsarin da aka kawo ba a yi masa kyakkyawan shirin ba.

Ana Fafutuka Da Tafka Dambarwa A Gaban Bankunan Najeriya
Ana Fafutuka Da Tafka Dambarwa A Gaban Bankunan Najeriya

Ana dai fargabar yiwuwar barkewar rikici, la'akari da yadda al'umma suka fusata a kan wa’adin da aka sanya wajen daina amfani da tsoffin kudin da aka canja a kasar.

Kazalika masana tattalin arzikin kasa na ganin kamata ya yi abi matakin daki-daki har sai al’umma sun gamsu kuma kudin sun wadata a kasar kamar yadda Dakta Isa Abdullahi ya yi mana bayani..

Baya ga wadanda suka yi cincirindo a harabar bankuna da dama a fadin kasar a yau, abin jira a nan shi ne ranar da za a yi zaman sauraron hukuncin da za a yanke domin kawo karshe matsalolin da tsarin ya haifar.

Saurari cikakken rahoto daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:

Duk Da Kara Wa’adin Canja Tsoffin Kudi ‘Yan Najeriya Na Ci Gaba Da Nuna Fargaba.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:10 0:00

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG