Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Douye Diri Ya Sake Lashe Zaben Gwamnan Jihar Bayelsa


Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri (Hoto: Duoye Diri Facebook)
Gwamnan Jihar Bayelsa, Douye Diri (Hoto: Duoye Diri Facebook)

Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Bayelsa na cike da farin ciki bayan da hukumar zabe ta INEC ta ayyana gwamnan jihar Douye Diri a matsayin wanda ya lashe zabe don wa'adi na biyu.

Hukumar zaben Najeriya ta INEC ta ayyana gwamnan jihar Bayelsa na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba, 2023.

Bayan kammala tattara sakamakon zaben kananan hukumomin jihar a cibiyar tattara sakamakon zabe ta jihar da ke birnin Yenagoa, baturen zabe Farfesa Kuta Farouq, ya ayyana Douye Diri a matsayin wanda ya lashe zaben don wa’adi na biyu.

Diri ya samu kuri'u 175,196 inda ya doke abokin hamayyarsa Timipre Sylva na jam'iyyar APC, wanda ya samu kuri'u 110,108, yayin da dan takarar jam'iitae Labour ya sami kuri'u 905.

Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar sun yi ta murna bayan da hukumar INEC ta fidda sakamakon zaben.

Yayin da jimlar wadanda suka yi rijistar kada kuri'a ya kai 1,570,862, kuri'u 372,000 aka tantance.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG