Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Donald Trump Ya Yiwa Kwamitin Kemfen Dinsa Garambawul


Donald Trump na jam'iyyar Republican dake takarar shugaban kasar Amurka
Donald Trump na jam'iyyar Republican dake takarar shugaban kasar Amurka

Dan takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump yayi garambawul ga kwamitin yakin neman zabensa, watanni uku kamin Amurkawa su zabi wanda zai gaji shugaban Amurka na yanzu cikin watan janairu mai zuwa.

Donald Trump ya nada Stephen Bannon, wani babban jami'i a wata kafar yada labarai a dandalin internet Breitbart, ya zama babban jami'in yakin neman zabensa, sannan ya karawa Kellyanne Conaway, mai aikin jin ra'ayoyin jama'a a zaman manajan kamfen dinsa.

"Mutanene da suka cancanta sosai, wadanda suke da sha'awar cin zabe,kuma sun san hanyoyinda za'a kai ga samun nasara," inji Mr. Trump kamar yadda yayi bayani cikin wata sanarwa da ya fitar.

Da akwai alamun kara sabbin masu bashi shawara biyu zai rage karfin shugaban kwamitin yakin neman zaben Mr Trump na yanzu watau Paul Manafort, wanda shine manajan kamfen din Trump tun bayan da dan takarar shugabancin kasar ya kori tsohon manajansa Corey Lewandowski cikin watan Yuni. Amma sanarwar da Mr Trump ya fitar tace sauye sauyen ba zasu shafi matsayar Mr. Manafort ba.

Manafort yana fuskantar zargi kan irin danganatakar dake akwai tsakaninsa da tsohon shugaban Ukraine mai ra'ayin Rasha Viktor Yanukovich.

XS
SM
MD
LG