Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Nazari Kan Koma Bayan Ilimi A Kasar Ghana-Kashi Na Daya-Nuwamba, 16, 2022


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Kamar yadda muka alkawarta, shirin Domin Iyali ya gayyaci masu ruwa da tsaki domin nazarin matakan shawo kan koma bayan harkokin ilimi a arewacin kasar Ghana, daya daga cikin kasashen yammacin Afrika da binciken Babban Bankin Duniya ya nuna hannun agogo na komawa da baya a fannin ilimi.

Bakin da muka gayyata sun hada da Malam Abdallah Tobodu, Koodinetan sashen ilmin addinin Musulunci na hukumar ilimi ta Ghana, da Gimbiya Ummul Khair Jafar ‘yar jarida kuma uwa, da Samira Yahaya AbdurRahman: Babbar jami’a a hukumar wayar da kan al’umma ta kasa (NCCE), da Issah Mairago Gibril Abbas mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum.

Saurari cikakken shirin cikin sauti:

DOMIN IYALI: Nazari Kan Koma Bayan Ilimi A Kasar Ghana-Kashi Na Daya
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:46 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG