Idan kuna biye da mu shirin Domin Iyali yana nazari kan cika shekaru takwas da aka yi ranar alhamis da ta gabatar da sace ‘yan matan Chibok 276 da har yanzu babu tabbacin inda sama da dalibai 100 su ke ko kuma halin da su ke ciki ba.
Wakiliyar Sashen Hausa, Madina Dauda ta tattauna da shugaban ‘yan asalin Chibok mazauna birnin tarayya Abuja Nkeki Mutah, da Madam Martha Bitrus Dalu ita ma ‘yar asalin Chibok wadda kuma ta rubuta littafi kan sace ‘yan matan.
Ga ci gaban bayanin na su.