Kwamitin zaben fidda gwani na masu neman kujerar gwamna a jihar Katsina ta ayyana Dakta Dikko Umaru Radda, dake zaman tsohon shugaban hukumar bunkasa kanana da matsakaitan sana’o’i wato SMEDAN a matsayin wanda ya sami nasarar lashe zaben fidda gwani na kujerar gwamnan jihar Katsina a karkashin inuwar jam’iyyar APC.
Radda ya sami kuri’u 506 inda ya kayar da abokin takararsa na gaf-da-gaf Mustapha Muhammad Inuwa wanda ya sami kuri’u 442.
Haka kuma baya ga Mustapha Muhammad Inuwa dake matsayi na biyu a zaben fidda gwanin da ya sami kuri’u 442, Abbas Umar Masanawa ya biyo bayansa da kuri’u 436.
Sauran sun hada da sanata Abubakar Yar’Adua wanda ya sami kuri’u 32, Faruk Lawal Jobe da ya sami kuri’u 71, Abdulkarim Dauda Daura da ya sami kuri’u 7, Umar Abdullahi Tsauri Tata ya sami kuri’u 8, Mannir Yakubu mai kuri’u 65, da Akitek Ahmed Dangiwa mai kuri’u 220.
Shugaban kwamitin zaben na jihar Katsina, Kaka Shehu, wanda ya bayyana sakamakon zaben a filin wasa na Muhammadu Dikko dake Katsina, ya ce daga cikin wakilai dubu 1 da 805 da aka zabo daga Unguwani 361 na jihar, su dubu 1 da 801 ne aka amince da su kuma aka sami kuri’u hudu kawai wadanda basu da ingancin da za’a kirga su a karshen zaben kamar yadda wakilinmu a jihar ya shaida mana.
Idan ba’a manta ba jimillar masu neman kujerar gwamna a zaben fidda gwanin jihar guda tara ne wadanda suka tsaya a wannan takarar don neman su gaji gwamna mai ci, Aminu Bello Masari kamar yadda muka ruwaito a baya.
Masu neman takarar dai sun hada da jami’an gwamnatin da ke ci a halin yanzu da kuma tsaffin jami’an gwamnati da ‘yan kasuwa.
Dakta Dikko Radda wanda ya lashe tikitin jam’iyyar shi ne tsohon shugaban hukumar bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu ta SMEDAN, Muhammad Inuwa wanda ya zo na biyu tsohon sakataren gwamnatin jihar ne, yayin da Masanawa wanda ya zo na uku ya kasance tsohon manaja daraktan hukumar kula da buga kudi ta Najeriya ne, sai mataimakin gwamna mai ci, Manir Yakubu.
Sauran wadanda suka nemi tikitin sun hada da tsohon kwamishinan kasafi da tsare-tsare, Faruk Lawal Jobe, tsohon babban daraktan bankin gine-ginen gidaje na ma’aikata a Najeriya, Akitek Ahmed Dangiwa, wani dan kasuwa mazaunin jihar Kaduna, Sanata Abubakar Yar’adua; Umar Abdullahi Tsauri Tata da kuma tsohon babban jami'in tsaro na shugaban kasa, Abdulkarim Dauda Daura.
A wani bangare kuma, kwamitin zaben fidda gwani karkashin shugabancin, Chika Nwozuzua, na masu neman tikitin kujerar gwamna a jam’iyyar PDP a jihar Katsina ya ayyana Sanata Yakubu Lado Dan Marke a matsayin wanda ya sami nasara a zaben da kuri'u 740.
Chika Nwozuzua ya bayyana cewa Danmarke ya sami kuri’u 740 inda ya doke abokin karawarsa, Salisu Yusuf Majigiri, wanda ya sami kuri’u 257, da wasu masu neman takarar biyu.
Sauran ‘yan takarar da suka hada da Ahmed Yar’Adua da Shehu Inuwa Imam, sun samu kuri’u 53 da 44, bi da bi.
A cewar Chika Nwozuzua, wakilai dubu 1 da 117 da aka zabo daga kananan hukumomin jihar 34 ne suka halarci zaben fidda gwanin da aka gudanar a hedikwatar jam’iyyar dake jihar Katsina.
A cikin duka wakilan dubu 1 da 117, su dubu 1 da 108 ne aka amince da su inda aka sami kuri’u marasa inganci 10, a yayin da wakilai hudu ba su kada kuri’a ba bayan amincewa da su.
Tuni dai matasa da suka fito daga jihar Katsina suka yi ta tofa albarkacin bakinsu kan yadda zaben fidda gwanin na jam’iyyar APC ya kaya, wasu na nuna farin cikinsu ga yadda gwamna Aminu Bello Masari ya bari aka yi adalci ga duk wanda ya tsaya neman takara a zaben fidda gwani na jihar da ya kai ga Dakta Dikko Radda samun nasara ba tare da nuna goyon baya ga kowanne dan takara ba duk da cewa mataimakinsa, Manir Yakubu, na cikin yan takarar ba.
Matasan dai na jinjinawa gwamna Bello Masari ne suna mai cewa ba’a taba yin zaben fidda gwani da aka yi adalci ta hanyar barin masu jefa kuri’a su kada kuri’ar su ba tare da matsa mu su a kan dan takara da ya kamata su zaba ba kamar wannan.
Idan ana iya tunawa ma sai da Dikko Radda ya yi kira ga uwar jam’iyyar APC a matakin jiha da tarayya da su yi adalci ga duk mai neman takara.