Bayan ganawarsu da shugaban Amurka Donald Trump, ‘yan majalisar dattijai na jam’iyar Republican sun bada tabbacin niyarsu ta kada kuria kan gagarumin tsarin haraji, a mako mai zuwa da zata zaftare harajin kamfanoni na dindindin, ya rage harajin da ma’aikata ke biya akan albshin su na dan karamin lokaci, ya kuma kara yawan bashin da ake bin Amurka da sama da dala triliyon daya.
Shirin da aka yi wannan makon shine a kada kuri’a a kan dokar harajin a majalisar dattijai” inji gagarabadau masu rinjaye John Cornyn na jihar Texas. “ manufar ita ce a sake zaburar da tattalin arzikin kasar.
A halin da ake ciki kuma, wani rikici ya barke a kan wanda ke da ikon fada aji a wani ofishin gwamnati jiya Litinin da ya kunshi wasikun email da shigar da kara da kuma bada kyautar fanke.
Babban jami’in kasafin kudi na fadar White House Mick Mulvaney da Leandra English da tayi aiki karkashin gwamnatin Obama dukansu suna ikirarin cewa, sune ke rike da mukamin matsayin mukadashin darektan cibiyar kare abokan huldar kasuwanci, kuma dukansu biyu sun tafi ofis da nufin kama aiki guda.
English, mataimakiyar datekta a cibiyar ta yiwa ma’aikatan ofis din barka da dawowa hutun cika ciki da ake kira Thanksgiving.
Nan da nan Mulvaney ya turawa ma’aikatan sakon email ya shaida masu suyi watsi da email din da English ta tura, su tura sakon zuwa ofishin bada shawarwari kan harkokin shari’a. su kuma je ofishinsa su ci fanke.
English tayi barazanar kai karar Mulvaney bisa ikirarin cewa, mukamin nata ne.
To amma Fadar White House tace doka a bayyane take, kuma tana goyon bayan Mulvaney. Tuni yake yin akin mukadashin,kamar shike shugabancin cibiyar.
Facebook Forum