Bayan tashin bam jiya a Abuja wakilin Muryar Amurka ya ziyarci daya daga cikin asibitocin da aka kai gawarwakin wadanda suka rasa rayukansu da wadanda suka jikata yau da asubahi.
Daga asibitin wakilinmu ya samu bayanai daban daban daga wadanda Allah Ya sa suna da sauran ruwan sha. Wani yace lokacin da abun ya auku bai san hannushi ya yanke ba. Da farko bai san ya rasa hannusa ba.
To amma ga babban editan New Telegraph bam din da ya tashi shi ya kawo karshen rayuwarsa. Ya je shagon da ake sayar da wayar salula a bakin kofar shiga plaza din sai bam din ya tashi. Nan take Allah Ya karbi ransa
Kafin ya fara aiki da jaridar New Telegraph Suleiman Bisallah mataimakin edita ne a jaridar Daily Trust. Babban editan Daily Trust Munir Dan Ali yayi magana akan marigayin. Yace da ya ji labarin ya girgiza matuka. Ranar Juma'a da ta gabata suka hadu a masallaci inda suna jajen rasuwar wani sai gashi tashi ma ta zo a tashin bam din Abuja.
'Yaruwar marigayin Aishatu Abdullahi Doma tace sun yi imani ga Allah duk mai rai mamaci ne. Tace babu abun da zata ce saidai addu'a kuma a tayata da addu'a Allah Ya karbi bakuncinsa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.