Rundunar da ke wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta tabbatar da mutuwar jami’anta uku a yankin karamar hukumar Barkin Ladi.
Kakakin rundunar tsaro ta “Special Task Force” a jihar, Major Umar Adam ya ce jami’an na su sun gamu da ajalinsu ne yayin da suke gudanar da aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.
“Yanzu dai komai ya lafa har mun karin ma’aikata…. don mu tabbatar ba a samu karaya na doka ba.” Inji Major Adam.
A cewar shi, dakarun sun gamu da ajalinsu ne yayin da suka je kai dauki a wasu hare-hare da aka kai a Barkin Ladi.
Tun kusan watanni uku kenan rikicin ya tsananta musamman a kananan hukumomin Barkin Ladi, Jos ta Kudu, Riyom da wasu sassan karamar hukumar Bassa.
Hon. Peter Gyenden, mamba mai wakiltar Barkin Ladi a Majalisar Dokokin jihar ta Filato,
“Ya ce batun kashe-kashe, sace-sace da barnata amfanin gonaki suke faruwa kusan kowacce rana, mutane ba sa zama a cikin hankalinsu a yanzu, ya kamata jami’an tsaro su dauki matakai domin hana aukuwar wannan abu,” a cewar Gyenden.
Sakataren kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Barkin Ladi, Abubakar Gambo, ya ce an kashe masu shanu an kuma kona wasu gidaje.
“Kwanakin baya akwai, satar shanu da aka yi a ka kuma kashe makiyayin, abin da na samu tabbaci a kai shi ne sojoji ke ta korar mutane suna ta harbi, sun ji wa mutane akalla 12 rauni.” Inji Gambo.
Kan korafe-korafen da alummomin ke yi kan jamian tsaron kuwa, kakakin rundunar tsaro na STF, Manjo Umar Adam ya ce suna gudanar da aikinsu ne bisa ka’idar da doka ta gindaya masu.
Saurari rahoton Zainab Babaji daga Jos:
Facebook Forum