Dr. Choguel Maiga ya na mai cewa ba sa shawara wajen daukan muhimman matakan gudanar da lamuran mulki, misalin yadda suka dage babban zaben kasar da ya kamata a gudanar a shekarar nan ta 2024 ba tare da tuntubar mambobin gwamnati ba, abin da ya ja hankulan masu sharhi kan harkokin siyasa a Nijar.
A yayin gangamin kungiyoyi da jam’iyyu mambobin kawancen M5 RFP da ya jogoranta a karshen mako a Bamako ne firai ministan Malin Dr. Choguel Maiga ya fallasa yanayin rashin shawarar da ake fama da shi a tafiyar gwamnatin rikon kwaryar kasar.
Ya ce "idan kuna tune da radin kanmu a ranar 26 ga watan Maris na 2022 muka kayyade cewa rikon kwarya zai kammala bayan watanni 24 wanda kuma a ranar 6 ga watan Yuni aka rattaba hannu kan dokar dake jaddada wannan mataki.
"abin nufi wa’adin gwamnatin ya kamata yazo karshe a ranar 26 ga watan Maris na bana, amma kuma wasu suka daga ranar ba tare da yin muhawwara a kan batun a gwamnatance ba.
Ko kun taba tsamanin haka na iya faruwa? Ni ma ta kafafen labarai na ji labarin dage wannan rana"a cewar firai ministan
Tuni kalaman Dr. Choguel Maiga suka haddasa mahawwara a tsakanin ‘yan Mali wadanda ke ganin ya yi dai-dai, da wadanda ke ganin bai kyauta ba.
Amma haka wannan batu ke daukan hankulan masu sharhi kan al’amuran yau da kullum.
To amma masani kan huldar kasa da kasa Moustapha Abdoulaye na hasashe kan cewa sabon matsayin na firaiministan Mali ba zai rasa nasaba da dabarun irin na gogaggun ‘yan siyasar da suka ga jiya suka ga yau ba.
Tun a ranar da Dr. Choguel Maiga ya yi wannan furici ‘yan Mali da dama ke jiran ganin an tsige shi daga mukaminsa, to amma masana na ganin ba a banza ba ake jinkirta yin hakan musamman idan aka yi la’akari da rawar da firai ministan ya taka wajen shimfida manufofin gwamnatin ta rikon kwarya.
Rahotannin daga kasar ta Mali dai na cewa an dage taron majalissar ministoci da ya kamata a gudanar a yau Laraba 20 ga watan Nuwamba.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna