Masu bibiyar lamuran siyasar jihar Kano sun ce wannan abin bai zo da mamaki ba.
A ranar Alhamis da ta gabata ne ofishin gwamnan mai jiran gado na Jam’iyyar NNPP ya fitar da wata sanarwa dake shawartar mutanen da gwamnatin mai barin gado ta baiwa plotai a wasu wurare da asalin su mallakar hukumomi ko cibiyoyin gwamnati ne da su dakatar da aikin gine-ginen a wuraren ba tare da bata lokaci ba.
Sa’o’i kalilan bayan fitar da waccan sanarwa, kwamishinan labaru na gwamnati mai barin gado Malam Mohammed Garba ya fitar da martani, inda ya ja hankalin gwamnati mai jiran gado cewa, Dr Abdullahi Umar Ganduje zai ci gaba da zama halastaccen gwamnan Kano har zuwa ranar 29 ga watan gobe na maayu, a don haka sai ya shawarci gwamna mai jiran gado ya dakatar da fitar da duk wata sanarwa da ta shafi harkokin gwamnati har sai an rantsar da shi.
Amma ga alama, gwamnan mai jiran gado bai karbi wannan shawarar ba, domin kuwa, ofishinsa ya sake fitar da wata sabuwar sanarwa, makamanciyar ta baya, inda a cikin ya yi gargadin cewa ba zai biya duk wani bashi da gwamnati mai barin gado ta ciwo ko zata ciwo daga ranar 18 ga watan jiya na Maris zuwa ranar 29 ga watan gobe na Mayu, kuma koda basussukan da aka ciyo a shekarun baya, zai musu garanbawul.
Yanzu haka dai masu kula da lamura sun fara tsokaci akan wannan dambarwa. Comrade Abdulrazak Alkali shugaban kungiyar OCCEN mai shalkwata a Kano, masu rajin shugabanci na gari ya ce babu shakka abin bai zo da mamaki ba, la’akari da yadda bangarorin biyu suka gudanar da kamfe na neman kuri’a ba tare da martaba juna ba gabanin zabe.
Shi ma Malam Kabiru Sa’idu Sufi, Malamin kimiyyar siyasa a kwalejin share fagen shiga Jami’a ta Kano ya ce abin da wannan dambarwa ke nunawa shine gagarumin banbancin dake tsakanin kudirce-kudirce da manufofin gwamnatocin biyu. A cewarsa, la’akari a nan shi ne, a duk lokacin da sabuwar gwamnati ta shigo al’amuran da ta fara fitar da sanarwa akan su hakan wata yar manuniya ce dake alamta cewa, sune zata bai wa fifiko, amma mutane za su yi tsammanin batun samar da ababen more rayuwa kamar ruwa da kiwon lafiya da ilimi za su kasance kan gaba a cikin abubuwan da zata baiwa kulawa.
A cewar Farfesa Nasiru Adamu Aliyu, mai lambar kwarewar aikin lauya ta SAN kuma Malami a Jami’ar Bayero Kano, kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayyana karara, gwamna mai barin gado zai ci gaba da tafiyar da al’amuran gwamnati da harkokin Jama’ar Kano har zuwa ranar 29 ga watan Mayu mai zuwa. Yana mai cewa, gwamna mai jiran gado bashi da hurumi akan kowane al’amari sai bayan ya yi rantsuwar kama aiki a ranar 29 g watan Mayu.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari cikin sauti daga Kano: