Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar NNPP Rabiu Musa Kwankwaso ya ba da tabbacin cewa ba zai rika yin shisshiga a gwamnatin Abba Yusuf da aka fi sani da Abba Gida-Gida Ba.
Yusuf shi ya lashe zaben gwamnan jihar Kano karkashin jam’iyyar ta NNPP wacce a wannan karon ne ta fara takara.
Kalaman Kwankwaso na zuwa ne yayin da ake ta rade-radin cewa shi ne zai rika jan ragamar mulkin jihar ta Kano ta bayan fage ba Abba Gida-Gida ba.
Sai dai yayin wata tattaunawa da manema labarai kamar yadda gidan talbijin na Channels ya ruwaito, Kwankwaso ya ce ba zai tsoma bakinsa a sha’anin gwamnatin Abba Gida-gida ba.
“Ko da mai shara ka nada a matsayin shugaba, bai kamata ka yi katsalandan ba. Idan ya nemi shawararka, sai ka ba shi.
“Amma kuma idan bai tambaya ba, sai ka yi shiru.” Kwankwaso ya ce a hira da manema labaran.
Sai dai Kwankwaso, wanda ya taba mulkar jihar ta Kano har tsawon wa’adi biyu, ya ce idan ya ga gwamnatin ta saki hanya dole ne zai yi magana.