Rashin gamsuwa da halaccin hanyoyin da Shugaban Jam’iyyar ta CPR-Inganci, Kasim Moukhtar ya bi wajen ɗaukar matakin rushe kwamitin gudanarwar jam’iyyar a reshenta na Yamai ne ya haifar da takun saƙa tsakaninsa da wasu gaggan muƙarraban jam’iyyar a yankin Yamai.
“Ba wani takarda aka bamu ba, ba wani aka turo da saƙo ya gaya mana ba, mun gani ne a yanar gizo ana yaɗa bayanin,“ inji Shugaban wannan jam’iyya a gundumar Yamai ta 3, Ibrahim Garba Barmu.
A cewar shugabannin reshen Yamai, girman matsalar da ake ciki yau a CPR Inganci, wani abu ne da ke barazanar tarwatsa wannan jam’iyyar, dalili kenan da suka buƙaci kwamitin ƙoli ya dakatar da shugabanta.
Shugaban reshen wannan jam’iyya a gundumar Yamai ta biyu, Adamu Garba. wanda aka sanar cewa an koreshi kwata-kwata daga jam’iyyar, ya lashi takobin ƙalubalantar wannan mataki.
"Haba jam'iyya kamar ta gado?Nashi ne shi kaɗai da kawai sai ya rubuta takarda?Wa aka ba takarda ya kawo min?Ni ban koru ba, ni dan inganci ne kuma ina jin kotu kaɗai ce za ta iya tsigeni daga jam'iyyar."
Shugaban jam’iyyar CPR Inganci na ƙasa, Kasim Moukhtar da na kira ta waya, ya bayyana cewa ba zai ce komai ba akan wannan batu.A cewarsa ba shi da muhimmanci a wurinsa, hasali ma ya hana in ambaci sunansa cikin wannan rahoto duk kuwa da cewa na fahimtar da shi cewa ƙa’idar aiki ba ta yarda da irin wannan buƙata ta sa ba.
Facebook Forum