Ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka dauki dogon lokaci ana tafkawa ya yi sandiyar mutuwar mutane takwas da akasarin su matasa ne a garin Rafin Gora dake cikin karamar hukumar Kontagora a jihar Niger.
Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Litinin wanda ya tayar da hankalin mazauna yankin ainun.
Masu aikin ceto na can suna neman wadanda suka bace.
Alhaji Abdullahi Ibrahim wani mazaunin garin ya bayyanawa sashen Hausa cewa akwai wasu, wadanda har yanzu ba’a gansu ba. Mutanen garin sun kidime saboda irin barnar da ruwan ya yi.
Kodayake duk kokarin jin ta bakin ‘yan sandan yankin da Sashen Hausa ya yi ya cutura amma ya zanta da shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Alhaji Ibrahin Inga wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Yace suna kokarin neman wadanda ba’a gansu ba. Idan akwai wadanda suke da rai zasu sani idan kuma sun rasa rayukansu, zasu nemo gawarwakin su. Cikin mutane takwas din da ya tabbatar sun rasu yace akwai wadanda ruwa ya tafi dasu akwai kuma wadanda gini ya rushe kansu. Amma har yanzu suna ci gaba da tantancewa domin su sanin ahihin abun da ya faru.
Hukumar bada agajin gaggawan ta umurci wadanda suke zaune a gabar rafin Koramu su kaura domin kaucewa ambaliyan ruwan.
A saurari rahoton Mustapha Nasiru Batsari domin jin karin bayani
Facebook Forum