A Najeriya, batun nuna sha'awar tsayawa takara da wasu Ministoci suka yi, ba tare da sun ajiye aikinsu ba, ya dauki hankalin masana harkokin siyasa har da kwararru a fannin shari'a.
Ya zuwa lokacin daukan wannan rahoto, ministoci biyu ne suka baiyana aniyar tsayawa takarar kujerar Shugaban kasa a zaben shekara 2023.
Akwai ministan sufuri, Chibuike Amaechi, da ministan kwadago Chris Ngige amma kuma duk ba su ajiye ayyukansu ba.
To wai, a ina gizo ke saka ne a kashi 84 karamin kashi na 12 a sabuwar dokar zabe da kuma tanadin kundin tsarin mulkin kasa?
Barista Mainasara Umar, masanin shari’a ne ya kuma duk wanda ya ke aikin gwamnati kuma yana karbar albashi kuma zai karbi pensho bayan ya yi ritaya, dole su yi murabus kwana 30 kamin ranar da za a jefa kuri'ar zabe.
Idan akwai sabani a kundin tsarin mulkin da sabuwar dokar zabe ta shekara 2022,
Mene ne ya ba wadannan Ministocin karfin gwiwar daukan matakin kin ajiye aiki alhali suna so su tsaya takara?
Kwararre a tsangayar siyasa kuma Malami a Jami’ar Abuja Dokta Farouk Bibi Farouk ya yi ya ce wannan hukunci da aka samo na Umuahia, Abia wanda ya ce a soke wannan dokar, komai raunin wannan hukuncin, sai wata kotu ta daukaka kara, ta yi watsi da wannan hukuncin sannan a fara amfani da wannan doka, komai kuskurin da alkalin ya yi, ba zama laifin wanda ya bi wannan dokar ba.
Amma ga mai nazari a al’amuran yau da kullum Abu Hamisu, yana ganin an yi wa dokar karan tsaye.
Abin jira a gani shi ne yadda za ta kaya a lokacin zaben fidda gwani da Jami'yyun kasar za su yi nan gaba kadan.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: