Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fom Din Takarar Shugaban Kasa Naira Miliyan 100 Ne - APC


Shugaba Muhammadu Buhari (tsakiya) a wajen taron majalisar zartarwar jam'iyyar APC A Abuja (Hoto: Fadar shugaban kasa)
Shugaba Muhammadu Buhari (tsakiya) a wajen taron majalisar zartarwar jam'iyyar APC A Abuja (Hoto: Fadar shugaban kasa)

Sai dai jam'iyyar ta APC ta ce, mata naira miliyan 30 kawai za su biya don sayen fom din nuna sha'awar tsayawa takara a maimakon miliyan 100.

Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta saka kudin fom din masu sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa akan naira miliyan 100.

A badi ne Najeriyar za ta gudanar da babban zabenta inda Shugaba Muhammadu Buhari zai kammala wa’adinsa na biyu.

Yayin wani taro da ta gudanar a ranar Laraba a Abuja, don duba shawarwari kan zabukan fidda ‘yan takara da za ta yi a matakan jihohi da na tarayya, jam’iyyar ta ce naira miliyan 30 zai zama kudin nuna sha’awar tsayawa takara yayin da shi kansa fom din kuma za a sayar da shi akan naira miliyan 70.

“Wanda yake so ya hau wannan babbar kujera ta shugaban kasar Najeriya, to zai cike fom din nuna sha’awarsa ya biya naira miliyan 30, sannan kuma fom din da zai nuna cewa yana so ya zama dan takara, shi kuma miliyan 70 ne , sai a karbi miliyan 100 kenan.” Darektan Watsa Labarai na Jami’yyar Salisu Na'inna Danbatta ya fadawa wakiliyar Muryar Amurka Medina Dauda bayan taron.

Zauren taron majalisar zartarwar jam'iyyar APC (Hoto: Fadar shugaban Najeriya)
Zauren taron majalisar zartarwar jam'iyyar APC (Hoto: Fadar shugaban Najeriya)

Sai da Danbatta ya kara da cewa, mata masu sha’awar tsayawa takarar shugaban kasa, za su sayi fom din nuna sha’awa ne kawai, wato za su biya naira miliyan 30 kenan.

“Abin da ka’ida ta nuna shi ne, akwai ita naira miliyan 30 din nan, ta nuna sha’awar yin kina so ki yi takara, ita kadai mata za su biya, wacce miliyan 70 wacce in namiji ne zai biya, an yafewa mata.” In Danbatta.

Zaman dai ya wakana ne karkashin jagorancin Shugaban kasa Mohammadu Buhari tare da goyon bayan Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, da Shugaban Jamiyyar Abdullahi Adamu da Gwamnoni da ma manya-manyan ‘ya'yan jammiyar.

Tuni dai tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, da mataimakain Shugaba kasa Farfesa Yemi Osinbajo da ministan sufuri Rotimi Amaechi wadanda duk ‘yan jam’iyyar ta APC ne suka riga suka bayyana aniyarsu ta neman shugabancin kasar.

XS
SM
MD
LG