Rahotanni sun nuna cewa batun iko kan ma'aikata yana daga cikin dalilan da suka sa Admiral na sojan ruwan Amurka Robert Harward, yaki karbar wannan mukami da aka bashi cikin makon jiya.
Harward shine mutum na farko da shugaba Trump ya zaba ya maye Michael Flyn wanda aka kora daga kan mukamin bayan kwanaki 24 kacal kan wannan mukami.
Shugaban na Amurka yana ganawa da mutane daban-daban su hudu kai tsaye wasu kuma ta wayar tarho a katafaren gininsa dake Florida da ake kira Mar-Largo dake kan gabar ruwa.
A halin da ake ciki kuma, Sanatoci biyu 'yan jam'iyyar Republican John MCcain mai wakiltar jahar Arizona da Lindsay Graham na jahar Carolina ta kudu, duk sun bayyana damuwa ko tababar shugaba Donald Trump yana da kwarewar gudanar da harkokin kasashen ketare. Musamman rashin kan gado a fadar shugaban kasa, da kuma alamun yana nuna sanyin gwiwa wajen tunkarar Rasha saboda katsalandan da ta yi cikin harkokin zaben Amurka. McCain, yace kawayen Amurka a Turai sun damu kan bayanai masu karo da juna da suke fitowa daga shugaba Trump.
Da yake magana a birnin Munich a wani taro kan harkokin tsaro Sanata Lindsey Graham, yace tilas sabon shugaban na Amurka yayi aiki da majalisar dokoki domin su ladabtar da Moscow.
"Shekara ta 2017 zata kasance shekarar da Rasha zata dandana kudarta a majalisar dokokin Amurka," Graham yayi ikirari.
Facebook Forum