TAHOUA, NIGERIA - Rikice-rikicen da suka biyo bayan girka sabon kwamitin gudanarwa na kungiyar daliban jami'ar Tahoua ne suka sa hukumar jami'ar gayyatar jami'an tsaro domin hana faruwar wani ta'adi tsakanin bangarori daban-daban na daliban makarantar.
Sai dai abin ya rikide izuwa arangama tsakanin jami'an tsaron da daliban jami'ar, da ta kai ga raunata daliban da ma shakar barkonon tsohuwa, kamar yadda shugaban kungiyar daliban jahar Tahoua SG Amadu Isufu Mohamed ya yi wa manema labarai bayani.
Rikici tsakanin daliban da ya samo asuli a lokacin zaben sabbin shugabanin kungiyar daliban USN ta jami'ar da ya kawo rarrabuwar kawuna tsakanin daliban da suka tashi baran-baran, tare da rarrabuwar kawuna, shine ya kai ga jami'ar neman gudumuwar jami'an tsaro, a cewar Dakta Hashimu Umma mataimakin shugaban jami'ar ta Tahoua.
Sai dai kungiyoyin fararen hula a wannan Jihar sun ce ba haka ya kamata a yi ba idan ana son a warware irin wannan matsalar cikin ruwan sanyi a cewar Alassane Abubakar shugaban kungiyar TLP (Tournons la page T.L.P).
Gwamnan Jihar Tahoua Issa Musa ne, ya shiga tsakani a wannan rikicin, abinda ya sa a ka saki dukkan daliban da a cafke kamar yanda Amadu Isufu Mohamed ya fada mana.
Yanzu dai kura ta lafa, kuma al'amura sun koma kamar yanda suke a can baya a jami'ar Tahoua.
Saurari rahot cikin sauti daga Harouna Mamane Bako: