Jihar dai tana fama da hare-hare yan bindiga da sace-sace a cikin yan shekarun nan, lamarin da yasa jihar ke da ‘yan gudun hijira a wasu sansanoni.
Rahotanni daga yankin karamar Hukumar Mariga na nuna cewa, yanzu kimanin kwanaki uku ke nan da wadannan ‘yan bindiga suka zagaye garuruwan Kuimo, Masabo, da kuma Sabon Wuri da ma wasu garuruwan da dama da ke wannan yanki.
A hirar shi da Muryar Amurka, wani mazaunin garin Kuimo da ya nemi a sakaya sunan shi ya ce mutanan suna cikin halin firgici, inda a ranar Talata nan sun harbi wani yaro tare da karya masa kafa kuma suna bin gida-gida suna tattara shanu da dama.
Ya kara da cewa, har zuwa yammacin ranar Talata 'yan bindigar na cikin daji kuma jami’an tsaro sun isa wurin amma duka mutane sun watse babu kowa a garuruwan.
Rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da kai wannan sabon hari, sai dai kwamishinan ‘yan sanda na jihar Neja, Monday Bala Kuryas, ya ce an kara tura karin jami’an tsaro a yankin kuma ya zuwa yanzu al’amurra sun lafa.
Ita ma gwamnatin jihar Neja ta ce tana sane da shigowar wadannan ‘yan ta’adda a wannan yanki kuma tana hada kai da jami’an tsaro domin shawo kan lamarin in ji Sakataren gwamnatin jihar Neja Ahmed Ibrahim Matane.
Wannan sabon hari dai tamkar wata sabuwar barazana ce a wannan yanki, musamman a dai-dai wannan lokaci da damuna ke kunno kai.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari: