Daliban da ke zanga zangar nuna adawa da yakin da Isra'ila ke yi da Hamas a jami'o'i a fadin Amurka, inda wasunsu suka yi arangama da ‘yan sanda, sun kafa sun tsare a yau Asabar kuma sun sha alwashin ci gaba da yin zanga zangarsu, yayin da sassan jami’o’i da yawa suka yi Allah wadai da shugabannin jami’o’in da suka nemi jami'an tsaro su fatattaki masu zanga-zangar.
Yayin da Jami'ar Columbia ke ci gaba da yin shawarwari tare da daliban da ke zanga zangar goyon bayan Falasdinawa a harabar makarantar da ke New York, majalisar zartarwar Jami'ar ta sanya hannu a wani kuduri a ranar Jumma'a wanda ya kafa wani kwamiti da zai yi bincike akan shugabancin jami’ar, wacce a makon da ya gabata ta kira ‘yan sanda don su wargaza masu zanga-zangar, lamarin da ya haifar da arangama ya kuma kai ga kamen mutane fiye da 100.
Duk da cewa Jami'ar ta sha sanya wa’adin tada dadalin masu zanga zangar ta kuma dage shi, Jami’ar ta aika da wani sakon Email ga dalibai a daren ranar Juma'a mai cewa sake kawo 'yan sanda makarantar "a wannan lokacin" ba zai yi tasiri ba, sakon ya kara da cewa suna fatan tattaunawar da ake yi zata kawo ci gaba.
Yayin da adadin wadanda suka mutu a yakin Gaza ke karuwa, masu zanga zanga a fadin Amurka na neman makarantu su yanke huldar kudi da Isra'ila su kuma kaurace wa kamfanonin da suka ce suna assasa rikicin.
Wasu dalibai Yahudawa sun ce zanga zangar ta na rikidewa ta koma nuna kyamar Yahudawa kuma suna fargaban shiga harabar makarantunsu.
Dandalin Mu Tattauna